Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dokokin Kamaru Tana Shirin Amincewa Da Dokar Ta Zarce Ga Mulkin  Paul Biya


Gwamnatin kasar Kamaru tana shirin dage ka’idar yawan wa’adin da shugaba zai yi kan mulki, matakin da zai bai ma shugaba Paul Biya damar sake tsayawa takara a shekarar 2011.

Jiya talata, kwamitin kula da tsarin mulki na Majalisar dokokin kasar ya amince da dokar -ta-zarcen. Har ila yau, wannan sauyin da za a yi ga tsarin mulki zai kuma kare shugaba Biya daga duk wata tuhuma bayan ya sauka daga kan mulki.

Mr. Biya ya shafe shekaru 25 ke nan yana mulkin kasar Kamaru. Shugaban babbar jam’iyyar adawar Kamaru ta SDF, John Fru Ndi, yace dokar ta bada Mr. Biya iko maras iyakaci.

Bacin rai dangane da shirin na Tazarce na daya daga cikin abubuwan da suka tunzura jama’a suka yi bore a karshen watan fabrairu. An kama daruruwan mutane.

XS
SM
MD
LG