Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dokokin Kenya Ta Yi Tayi Zaman Muhawara Kan Dokar Daunin Iko


Majalisar dokokin kasar Kenya ta yi wani zama yau domin yin muhawara kan daunin iko, da ake sa ran zai kawo karshen rudamin da ya biyo bayan zaben shugaban kasa. Yan Majalisar zasu tattauna kan wadansu kudurori biyu da ake bukata domin kafa doka a kai, da ya hada da yiwa kundin tsarin mulkin kasar gyaran fuska.

shugabannin Majalisar sun ce suna kyautata zaton yan Majalisar zasu amince da kudurin ya zama doka. Sai dai an sami koma baya a yarjejeniyar jiya Litinin yayinda babban jami’in ma’aikatun gwamnatin kasar Kenya ya shawarta cewa yarjejeniyar ta ba shugaba Mwai Kibaki karfin iko fiye da Prime Minista.

Jamiyar Orange Democratic Movement, ta sa hannu a yarjejeniyar da begen shugabanta Raila Odinga, zai rike sabon mukamin Prime Minista da aka kirkiro, mai iko daidai da shugaban kasa. Shugabannin jam’iyar ODM sun yi watsi da wannan shawarar ta babban jami’in ma’aikatun gwamnatin da cewa yana shiga sharru ba shanu kasancewa yana neman yin katsalandan a aikin Majalisa da jam’iyun da suka tsaida yajejeniyar.

XS
SM
MD
LG