Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Taraiyar Najeriya Ta Zabi Sabon Shugaba


A ranar Alhamis Majalisar wakilan Najeriya ta zabi Oladimeji Bankole, daga Jihar Ogun, a matsayin sabon Shugaban majalisar, kwana biyu bayan da tsohuwar Shugabar, Patricia Olubunmi Etteh tayi murabus.

An kuma zabi Usman Bayero Nafada daga jihar Gombe a matsayin Mataimakin Kakakin majalisar, ba tare da wata hamayya ba.

Abin da ya raba Etteh da mukaminta dai shine rahoton wani kwamitin bincike da ya sameta da laifin bada kwangilar sama da naira miliyan dari shida, ba tare da bin ka’ida ba.

Haka kuma majalisar ta rushe ilahirin shugabancin majalisar na Jam’iyya mai mulki ta PDP, kuma sai a nan gaba za a sake sabbin nadi. Mutane dai suna ta sharhi a kan murabus din da tshohuwar Shugabar tayi, inda yawanci suka baiyana farin cikinsu da yadda rikicin Majalisar ya kare a ruwan sanyi.

XS
SM
MD
LG