Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Man Fetur Ya Karye A Kasuwannin Duniya


Farashin gangar danyen man fetur din fa sami ragin centi 67 a kasuwar kadarori ta New York, inda yanzu ya dawo dollar 69 da centi 87.

Farashin danyen man ya fara faduwa ne tun daga lokacin da tsoro ya yawaita cewa kokarin kasashen duniya na tallafar tattalin arzikinsu ba zai yi wani tasiri na a zo z gani ba, wanda a karshe kuma, zai iya rage bukatun man daga kasashen.

Faduwar darajar man ta baya-bayan nan, ta faru ne saboda bayani da Ma’aikatar Makamashi ta Amurka ta bayar cewa ta sami karin wadatar mai a cikin gida, inda yanzu take da ganga miliyan 308 a ajiye.

A yau din dai, Kungiyar Kasashe Masu Arzikin Man Fetur ta OPEC, tace zata kira wani taron gaggawa domin tattauna wannan faduwar darajar da man fetur ke fuskanta. Ranar 24 ga watan nan na Oktoba za a gudanar da wannan taro, maimakon watan Nuwamba da aka tsara taron tun da fari.

Ana sa ran taron zai iya rage yawan man da kasasshen ke hakowa, domin rage karyewar darajarsa a kasuwar duniya.

XS
SM
MD
LG