Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Manyan bankunan Duniya Sun Rage Kudin Fito Domin Hana Tattalin Arziki Durkushewa


Manyan Bankunan kasashen duniya suna rage kudin fito a matakan hadin gwiwa da suke dauka da nufin hana mummunar durkushewar tattalin arzikin Duniya.

Babban Bankin Amurka ya bada sanarwar rage kudin ruwa cikin gaggawa da ya dauka Laraba,mataki da fadar White House ta bayyana goyon bayan ta akai.

Babban Bankin Tarayyar Turai,da na Ingila,Canada,Switzeland,Sweden,China duk sun bayyana niyar rage kudin ruwa da suke caji. Gwamnatin Ingila ta dauki matakin maida wani bangaren manyan Bankunan dake Britaniya karkashin ta. Fri-Minista Gordon Brown, yace anyi makonni ana aiki kan wannan shiri,ganin rudani da ake fuskanta Duniya baki daya,yace ya zama wajibi a bayyana shirin ahalin yanzu.Akwai cikakken bayani kan garambawul da matakan daidaitawa da muka dauka,kuma akwai sabbin dabaru ciki. An tsara shirin ne da nufin maido da yarda da kwarin gwiwa a sashen kudi,bugu da kari zai aza Bankunan Britaniya kan harsashi mai karfi,samarda kuzari domin gaba wajen taimakawa ayyukan yi,da bunkasa a ta ko wani fanni na tattalin arzikin mu.

Babban Bankin Japan yace bazai rage kudin fitoba,sai dai yace yana da cikakken goyonbaya ga matakan da takwarorinsa ya dauka.

XS
SM
MD
LG