Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Manyan Kasashen Duniya Sun Nace Sai Sun Musgunawa Iran


A ranar Talatar nan manyan kasashen duniya ke kwamba a birnin Berlin na kasar Jamus don tattauna karin matakan kuntatawa da zasu dauka akan Iran kan makaman nukiliyar da suke zargin cewa tana neman ta kera.

Mahalartan wannan taron, ko bayan ministan harakokin wajen jamus din, zasu hada da dukkan wakilan kasashen dake da mazaunin dindindin a kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya – watau Amurka, Ingila, Faransa, Rasha da China.

Wani jami’in diplomasiyar Faransa da bai son ace ga sunansa, ya tabattarda cewa wadanan kasashen na niyyar shata daftarin kuduri kargafawa Iran wani sabon takunkumi, a karo na ukku.

Ya kuma ce mai yiyuwa ne a kamalla hada hancin wannan kudurin, har ma a iya gabatarda shi a gaban kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya din kafin karshen wannan watan.

Daman dai Majalisar Dinkin Dduniya ta riga ta sawa Iran tarnaki har sau biyu saboda Iran taki barin sarrafa ma’adinin uranium – wanda ake iya hadawa da shi, a kera makaman nukiliyar.

Sai dai a inda aka fiton nan, Rasha da China sun nuna basa goyon bayan duk wani matakin matsin lamba kan Iran, to amma Amurka da kawayenta na ci gaba da zama daram kan bakansu na cewa Iran na ci gaba da neman fasahar kera makaman nukiliya, zargin da Iran ta sha musantawa

XS
SM
MD
LG