Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Manyan Kasashen Turai Suna Taron Duba Lamarin Iran


Taron ya hada da kasashe biyar masu ikon hawa kujerar naki a kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya, wato Amurka, Birtaniya, Faransa, Rasha da China, sai kuma Jamus da aka dan kara ta a wannan taron.

Kasar farisa dai tayi biris da wa’adin da aka bata na ta dakatar da inganta makamashin uranium ya zuwa satin nan na karshen Fabrairu, ko kuma a kara tsaurara takunkumin da aka kakaba mata a watan disamban da ya wuce.

Kasashen yammacin turai dai na zargin Farisa da kokarin mallakar makaman nukiliya, zargin da tuni Tehran ta musanta. Wani mai magana da yawun Prime Ministan Ingila, Tony Blair, ya gargadi Kasar farisa da kada ta dauka babu hadin kai tsakanin kasashen duniya, na kyamar wannan shiri nata na nukiliya.

Amma kuma Ministan Harkokin Wajen Rasha, Sergi Lavrov, yace Moscow ta damu da kurarin farmakin soja da ake ta faman yiwa kasar ta Farisa.

XS
SM
MD
LG