Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masu Kishin Islama A Somalia Sun Kwace Baidoa


Kungiyar ‘yan tawayen Somalia ta Al Shabab ta kame garin Baidoa, inda Majalisar kasar take.

Shaidun gani da ido sunce a yau Litinin Kungiyar ta karbe ragamar garin, ‘yan sa’o’i kadan bayan janyewar dakarun Habasha, wadanda dama sune ke kare gwamnatin kasar mara tagomashi.

Mazauna garin dai sunce an gwabza fada kafin mayakan kungiyar su sami nasara, koda yake dai babu bayanin wadanda suka jikkata.

Yawancin ‘yan Majalisar kasar dai suna Djibuti, makwabciyar kasar ta Somalia, inda suka je domin yin wani zama na musamman da aka bude a jiya Lahadi.

A yau ‘yan Majalisar suka amince da kara yawan kujerun Majalisar zuwa 550, domin cika wata yarjejeniya da gwamnati ta cimma da masu sassaucin ra’ayi.

XS
SM
MD
LG