Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mataimakin Shugaban Amurka Dick Cheney Zaiyi Shawarwari Da Sarki Abdullah NA Saudi Arabia kan hanyoyin Daidaita kasuwar Mai Ta Duniya2008-03-21-voa1


Ana sa ran mataimakin shugaban Amurka Dick Cheney zai zanta da Sarki Abdullah na Saudi Arabiya bisa hanyoyin daidaita kasuwar mai ta Duniya. Yau Jummaa ce Cheney ya isa Saudiyya bayan ya kai ziyarar ba zata Afghanistan.

Haka kuma Jami’an Amurka sunce Cheney zai karfafawa Saudiyya gwiwar kara kusanta da hulda da Iraqi domin karya lagon bunkasar martabar Iran cikin yankin. Saudiyya da wasu kasashen larabawa har yanzu basu tura jakadu Bagadaza ba.

Jiya Alhamis a Afghanistan Cheney ya gana da shugaban kasar Hameed Karzai.Shugabanin biyu sunyi kira ga kasashe dake cikin kungiyar kawancen tsaro ta NATO su karfafa alkawari da sukayi na taimakawa Afghanistan ta yaki tsageru,kuma ta farfado daga yaki da ya durkusadda kasar.

Cheney yace akwai bukatar Amurka da NATO su samarda wadatattun sojoji a Afghasnistan domin tinkararar kungiyar Taliban da take farfadowa da kuma al-Qaida. Mr. Karzai yace Afghaistan zata ci gaba da dogara kan sojojin NATO har sai ta sami karfin kare kanta.

XS
SM
MD
LG