Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matashi Rajoelina Ya Zama Shugaban Madagascar


Kotun Tsarin Mulki ta Madagascar, ta tabbatar da Andry Rajoelina a matsayin Shugaban kasa na riko, a kasar dake tsibirin tekun Indiya.

Kotun ta yanke wannan hukuncfi ne kwana daya bayan Rajoelina ya ayyana kansa a matsayin Shugaban kasa, tare da goyon bayan soji.

A karkashin tsarin mulkin kasar dai, shekarun Rajoelina sun gaza na yadda zai iya zama shugaban kasa.

Rajoelina yace zai kafa gwamnatin wucin gadi, wacce zata shirya zabe nan da shekaru biyu.

Ya maye gurbin Shugaba marc Ravlomanan ne, wanda ya sauka daga kan mukamin, ya kuma mika mulki ga hannun sojoji, bayan anyi watanni ana fama da tashe tashen hankula a titunan kasar.

To amma maimakon su karbi mulkin, sai sojojin suka mikawa shugaban 'yan hamayya Rajoelina ragamar, dama kuma shine yayi jagorancin boren da aka yi ta yi.

XS
SM
MD
LG