Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rasha Tayi Kira Da A Dauki Mataki Bai daya Da zai Hana Rudanin Tattalin Arziki


Shugaba Dmiry Medvedev na Rasha yace hanya guda za’a iya kauda rinchaɓewar tsarin tattalin arzikin Duniya shine a haɗa kai a aɗauki mataki guda da za’a yiwa tsarin kwaskwarima.

Kamfanin dillancin labarun Rasha ya bada labarin cewa shugaban na ƙasar Rasha yace zai ƙoƙarta gabatar da wannan shawarar tasa a gaban shugabannin ƙasashe ashirin masu arzikin masana’antun duniya daza’a yi a birnin Washington, DC, yace wajibi ne a ƙirƙiro sabon tsari, a kuma rage yawan dogaron da cinikayyar ƙasa da ƙasa keyi a kan Dolar Amurka.

A halin da ake ciki wata ƙididdigar cinikayya da sayen kayan da Amerkawa keyi, ta zama ma’aunin da ƙasa da ƙasa ke auna ƙarfin tattalin arzikinsu, alƙaluma sun nuna samun koma baya sosai a watan Satumba, kuma ma’aikatar cinikayyar Amurka ta bada rahoton samun babban koma baya a harkokin cinikayya, kuma yawan Amerkawan dake karɓar kuɗin ɓatarwa daga hukuma yanzu ya haura miliyan uku.

Kazalika, rahotanni na cewa an sami karayar tattalin azriki a ƙasar Jamus, ƙasar da ita ce tafi kowace ƙarfin tattalin arziki a nahiyar turai saboda ’yan Jamus sun rage yawan sayen kayan masarufi da suke yi. Jami‘an ma‘aikatar cinikayyar Jamus suka ce an sami raguwar cinikayar ’yan koli da kashi biyu daga cikin ɗari a watan Satumban da ya gabata.

Wannan rahoton ya girgiza kasuwannin shunkun Asiya domin alƙaluman hannayen jarin Nikkei a Japan sun yi ƙasa da kashi biyar daga cikin ɗari. Kazalika alƙaluman hannayen jarin kasuwannin Hong Kong, da London da kuma Paris duk suna jin jiki.

XS
SM
MD
LG