Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ministocin Gamayyar Turai  da Kungiyar Hada Kan Afirka Suna Taro a Ghana


Ministocin Gamayyar Turai da Kungiyar Hada Kan Afirka Suna Taro a Ghana domin tsara ajendar taron koli tsakanin kasashen kungiyoyin biyu, a Portugal, da ake sa ran yi cikin watan Disemba mai zuwa.

Ministocin suna muhawara kan ko shugaban kasar Zimbabwe zai halarci taron kolin, ko kuwa za a hana shi.

Wani dan jarida Kwafi Kpodo, da ya halarci taron na yau Laraba a Accra, yace jami’ai sun jaddada bukatar kungiyoyin biyu suyi aiki tare wajen ganin anyi taron, da kuma cimma guri daya.

Ana bayyana fargabar cewa rashin jituwa gameda gayyatar shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe zuwa taron kolin, zata kai ga sawa a fasa taron da ake son yi a birnin Lisbon, na Portugal.

Prime Ministan Brititaniya yace ba zai halarci taron ba idan shugaban Zimbabwe ya je, duk da haka,wani jami’in Portugal ya tabbatar cewa zaa gayyaci Mr. Mugabe .

XS
SM
MD
LG