Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Akalla Mutane talatin Sun Halaka A Iraqi.


Jami‘an tsaron Iraqi sun bada rahoton cewar harin boma-bomai a biranen Bagadaza da Mosul sun halaka mutane aƙalla Talatin a yau litinin.

Jami‘an tsaron suka ce mutane goma sha biyar ne suka halaka a harin birnin Bagadaza, sannan 45 suka jikkata lokacin da bom ya tashi a cibiyar horas da kuratan ’yan sandan Iraqi.

A can birnin Mosul kuma harin ƙunar baƙin wake na mota ya kashe mutane gomasha biyar, Talatin suka jikkata, jami’an Iraqi suka ce ga dukkan alamu ɗan ƙunar baƙin waken ya nufi wasu motocin sintirin sojin Amurka ne.

Jakadan Majalisar Dinkin Duniya na musamman a Iraqi, yayi gargaɗin cewa idan ba’ayi hattara ba, hare-haren da ake yawaita kaiwa ka iya janyo cikas a zaɓen majalisun gundumomin da za’a yi farkon shekara mai zuwa.

XS
SM
MD
LG