Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Barack Obama da John McCain Zasu Kara A Muhawarar Su Ta Karshe Daren Laraban Nan


‘Yan takarar shuagabancin Amurka,John McCain,da Barack Obama, zasu yi muhawarar su ta karshe ta talabijin a daren yau Laraba,ana kasa da mako uku kamin ayi zaben shiga fadar white House.

A karawar ta yau da za a yi a harabar Jami’ar Hofstra, dake New York, ana sa ran batun komadar tattalin arziki shi zai fi dauke hankali,batu da ya taimakawa Obama ya sami bude tazara tsakanin sa da abokin hamayyar sa na Jam’iyyar Republican a kasa baki daya, da kuma wasu jihohi dake da muhimmanci ga samun nasara a lokacin zabe.

Sakamakon kididdigar neman jin ra’ayin jama’a da gidan talabijin na CBS da jaridar New York Times suka kaddamar, ya nuna Obama kan gaba da kashi 53 cikin dari yayinda McCain kuma yana da kashi 39 cikin dari.Wata kididdigar da kamafanin dillancin labarum Reuters,da tashar talabijin ta C-SPAN,da kamfanin neman jin ra;ayoyin jama’a, Zogby,suka gudanar, ya nuna Obama yana kan gaba da maki hudu kacal.

Ana sa ran Mccain da Obama zasu gabatar da kansu a kowanne cewa shine yafi dacewa wajen fiddo da Amurka daga rikicin tattalin arziki da take fuskanta.

XS
SM
MD
LG