Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Musulmi Matasa A Birtaniya Sunfi Magabatansu Kishi  Inji Bincike


Binciken da wani kamfani mai ra’ayin ‘yan mazan jiya ya gudanar, ya nuna cewa hudu daga cikin matasa musulmi goma, masu shekaru tsakanin 16 zuwa 24 a Birtaniya, sunfi kaunar rayuwa karkashin tsarin shari’ar musulunci, fiye da dokokin irin na Birtaniya. Wannan ya ninka yawan musulmin da shekarunsu suka haura hamsin da biyar, da suka gwammace rayuwa karkashiun tsarin shari’ar musulunci, fiye da ta Birtaniya.

Kashi 13 bisa dari na matasa musulmi sunce suna sha’awar kungiyar Al-kaida da sauran kungiyoyin gwagwarmaya, amma kashi uku ne kawai na dattawansu suke da wannan ra’ayi.

Haka kuma, binciken ya nuna cewa kashi uku bisa hudu na musulmi matasa a Birtaniya sunfi son matansu su sanya hijabi, amma amma ko kashi daya bisa uku na tsofaffi ba a samu da wannan ra’ayi ba.

Daya daga cikin wadanda suka gudanar da wannan bincike, Munira Mirza tace manufar gwamnatin Birtaniya, kan al’adu mabambanta, ta kara lalata al’amuran zaman tare a Birtaniya. Tace kamata yayi gwamnatin Birtaniya tafi bada fifiko wajen mu’amala da da musulmi a matsayinsu na ‘yan kasa kamar kowa, maimakon maida hankalin da take yi wajen la’akari da bambance bambancen dake tsakaninsu.

XS
SM
MD
LG