Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Barack Obama Ya Bayyana Mutane Da Ya Nada Cikin Majalisar Tsaron Kasa.


Jami‘an jam’iyyar Democrat ta Amurka sun bada labarin cewar shugaba mai jiran gado Barack Obama ya bayyana tawagar jami‘an harkokin tsaron ƙasa a yau litinin, daga cikin manyan jami‘an da aka bada sanarwar naɗawa harda Hillary Clinton da aka miƙawa ma’aikatar harkokin wajen Amurka.

Ana kuma kyautata cewar Robert Gate zai ci gaba da riƙe muƙaminsa na sakataren ma’aikatar tsaron Amurka. sauran manyan jami‘an da aka bayyana muƙaman nasu sun haɗa da Gwamnan jihar Arizona Janet Napolitano, tsaron gida, sai kuma Susan Rice Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya da kuma Eric Holder, da aka nada jagoran ma’aikatar shari’a kuma Atoni-Janar na Amurka.

XS
SM
MD
LG