Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Ta Lashe Gasar Kwallon Kafa Ta Matasan Duniya


Sun sami wannan nasara ne a bugun daga kai sai gola, wanda ya basu damar lashe kofin duniya na matasa ’yan kasa da shekara goma sha bakwai.

Wannan ne karo na hudu tarihin wasannin kwallon kafa 12 na ’yan kasa da shekaru 17, da bugun daga kai sai gola ke raba gardama, ya yanke cewa ga wadanda su ka lashe kofin duniya.

Kungiyoyin kasashen biyu sun yi mintoci 90 na ka’idar wasa da kuma mintoci talatin na karin lokaci babu wanda ya zura kwallo a raga.

Dan wasan Spain da ya fara bugun daga shi sai gola, sai ya harba ta waje, sdaga nan kuma mai gadin ragar Najeriya Oladele Ajiboye ya hankade kwallon da ’yan wasan Spain biyu na baya da shi suka buga.

A bangaren Najeriya kuwa, Matthew Edile da Daniel Joshua da Ganiyu Oseni su suka jefa na su kwallayen, hakan ya ba Najeriya nasara da ci uku ba ko daya.

Sakamakon ya kara sanyaya gwiwar ’yan wasan Spain, wadanda har sau ukku suna kaiwa wasan karshe, ba tare da samun nasarar daukar kofin duniya ba.

A can baya ’yan wasan Najeriya ’yan kasa da shekara 17 sun taba lashe gasar a shekarun 1985 da 1993. Haka kuma, Jamus ta gama da Ghana a wasan neman matsayi na uku da ci biyu da daya, Alexander Esswein shi ne ya jefa kwallon da ya ci a karin mintocin cike lokaci.

XS
SM
MD
LG