Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Tana Daukar Matakan Hana Barnar Dukiyar Kasa


Matakin yana daga cikin kokarin da ake yi na kakkabe rashawa a sashen man fetur din kasar, inda Najeriya ke asarar miliyoyin daloli a ko wacce shekara sakamakon rashawa da cin hanci.

Shugaba Umaru Musa ‘Yar Aduwa, ya kafa wata hukuma da zata aiwatar da wannan shiri na sake tsarin kamfanin. Ya baiwa hukumar ikon rushe kamfanin NNPC, da kuma maye gurbinsa ta kamfanonin guda biyar, kamar yadda wani kwamiti da aka kafa shekaru bakwai da suka wuce ya bayar da shawara, kan yadda za a daidaita tsarin sashen sarrafa albarkatun man fetur.

A halin da ake ciki kuma, Hukumomin Najeriyar sun tsawaita wa’adin dokar hana yawon daren da aka kafa a birnin Fatakwal har sai illa ma sha Allahu. Saidai an rage tsawon awoyin da dokar zata yi aiki.

Hukumomi sun kafa dokar hana yawon daren sati biyu da suka gabata, bayan musayar wuta ta tsananta tsakanin sojoji da wani gungun bata gari, wanda yayi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.

Da farko dokar ta hana yawon daren tana farawa daga karfe bakwai na yamma zuwa shida na safe, amma yanzu ba zata rika farawa ba sai tara na dare. Hukumomin sun ce za a ci gaba da aiwatar da dokar, saboda a sami sukunin kara tabbatar da dauwamar nasarar da aka samu wajen maganin bata garin.

XS
SM
MD
LG