Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Tana Shirin Sayar da Wani Kaso  Daga Rijiyoyin Mai Dake Doron Kasa Da Cikin Teku


Wani babban jami’in Gwamnatin Nigeria ya bayyana cewar Gwamnatin Nigeria na shirin sayar da wasu daga cikin kason rijiyoyin manta da aka kiyasta samun ganga miliyan dubu biyu, nan ya zuwa karshen wannan shekara.J

iya Talata aka ji babban mai baiwa shugaban kasa shawara kan makamashi, Emmanuel Egbogah yana shaidawa manema labarai cewa za’a yi gwanjon rijiyoyin man dake gabar teku da wadanda ke cikin ruwan teku.

Ana kyautata cewar Kasar China zata zama a sahun gaban wadanda ke bukatar sayen rijiyoyin man na Nigeria.

XS
SM
MD
LG