Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nejeriya Tana Karbar Bakuncin Kasashe 60 Na Nahiyoyin Africa Da Kudancin Amurka


Fiye da shugabannin kasashen duniya sittin ne ke hallara a Abuja, fadar Gwamnatin Najeriya domin halartar taron farko na Shugabannin Kasashen Africa da Kudancin Amurka, wanda za a bude gobe Alhamis.

Wakilan Muryar Amurka a Abuja sun aiko mana da rahoto a kan wannan taro, inda suka ce tattauna hanyoyin hadin kai tsakanin nahiyoyin biyu, shine zai fi daukar hankalin taron, a wannan lokaci da kasashen Latin America, kamar su Brazil da Venezuela ke kokawar samun gindin zama da nahiyar turai, wadda aka ce ita ce ta gano Africa.

A yanzu dai, Shugaba Hugo Chavez na Venezuela ya kusan ninka yawan ofisoshin jakadancin kasarsa a sassa dabam dabam na wannan nahiya, tun daga shekarar 2005. Shi kuwa Shugaban Brazil, Luiz Inacio Lula Da Silva, ya ziyarci kasashen Africa har sau biyar daga shekarar 2002 zuwa yau.

Ya kuma taba karbar bakuncin wani taron shugabannin kasashe uku daga nahiyoyi dabam-dabam, wato Thabo Mbeki na Africa ta Kudu daga Africa, da Prime Minista mammohan Singh na Indiya daga Asiya, da kuma kasarsa ta Brazil daga Kudancin Amurka. Cinikaiya tsakanin Africa da Brazil kuwa, ta ninka tun a shekarar 2003.

Najeriya ma tace ciniki tsakaninta da Brazil ya kai kusan dalar Amurka miliyan dubu biyar a bara. Wani mai Magana da yawun taron, Akerodolu Olabanji, ya dan gutsuro kadan daga cikin abubuwan da za a tattauna, inda yace manyan batutuwan da za a tattauna dai sun hada da zuba jari, makamashi, ma’adinai da sauransu.

Yace babban al’amari dai shine na hadin kai, domin wannan taro kamar na gwaji ne, a sami wata hanya da za a hade hancin nahiyoyi biyu. Olabanji yace yana ganin zasu tattauna abubuwa da dama.

XS
SM
MD
LG