Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Bindiga A Yanmkin Niger Delta Sun Kaiwa Kamfanin Shell Hari.


Hukumomin Nijeriya sun ce ’yan bindiga sun kai hari a kan wani kwale-kwalen soja dake gadin wata tashar famfon mai ta kamfanin Shell.

An kai wannan farmakin yau Jumma’a a mashigin ruwan Nembe dake Jihar Bayelsa a kudu maso yammacin kasar. Suka ce babu abinda ya samu tashar famfon man ta Shell. Hare-hare sun zamo ruwan dare a yankin Niger Delta, inda ake da masana’antar mai da gas mafi girma a nahiyar Afirka.

A ranar alhamis, rundunar sojojin Nijeriya ta ce ta fatattaki wani harin da aka kai da karamin kwale-kwale mai gudu a kan wata tashar lodin mai ta kamfanin man Amurka mai suna Chevron. Wannan harin ya zo a bayan da babbar kungiyar ’yan tsageran yankin MEND ta ce ta yi harbi a kan wani jirgin soja mai saukar ungulu. Kungiyar ta ce tana son a ba mutanen yankin karin kason mai.

XS
SM
MD
LG