Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Obama Ya Fara Tunkarar Tattalin Arziki


A yau Juma’a Shugaban Amurka mai jiran gado yake ganawa da manyan mashawartan sa kan tattalin arziki, bayan nan kuma yayi taron manema labarai.

Shugaba Obama wanda ke shirin karbar ragamar shugabanci nan da makonni goma, zai gaji tattalin arziki cikin mummunan yanayin da bai taba shiga ba tun shekarun 1920.

Ana dai ta rade-radin wadanda zai nada su rike muhimman ma’aikatun kasar, ciki har da Sakataren Baitulmali. Dama a jiya Alhamis ya baiyana nadin Rahm Emmanuel, dan Majalisar Wakilai daga mazabar Illinoiis, a matsayin Shugaban Ma’aikatan Fadar White House.

Jiya Alhamis din dai ta kasance ranar hutu a kasar Kenya, domin murnar nasarar Obama, inda aka rufe cibiyoyin kasuwanci da na gwamnati, su kuma ‘yan koli suka rika sayar da singileti, da bajo, da huluna da sauran abubnuwa masu dauke da hotunan Obama.

Rahotanni daga asibitocin Kenya kuma sunce yawancin yaran da ake haifa a wannan lokaci, ana rada masu sunan Obama ne, ko na matarsa Michelle.

An dai ce kakarsa ta wajen uba, ta baiyana aniyarta ta zuwa nan Amurka, domin halartar bikin rantsar da shi a ranar 20 ga watan Janairu.

A jiya Alhamis Obama yayi magana da shugabannin kasashen duniya tara ta wayar tarho, wadanda suka bugo domin su taya shi murna. Shugabannin sun hada da na Australia, da Birtaniya, da Canada, da Faransa, da Jamus, da Isra’ila, da Japan, da Mexico da Korea ta Kudu.

XS
SM
MD
LG