Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar kasashen masu arzikin mai ta tsaida shawar rage yawan mai


Kasar Saudiya ta bayyana cewa kungiyar kasashen masu arzikin mai ta tsaida shawar rage yawan mai da take haka da kimanin ganga miliyan biyu a rana bayan wani zama da kungiyar tayi a Algeria. Ministocin harkokin mai na kungiyar sun yi kira da a rage yawan mai da ake haka domin daidaita farashin mai da ya fadi da sama dad ala 100 ganga tun watan Yuli.

Ana kyautata zaton za a bada sanarwa ta musamman dangane da wannan batun zuwa wani lokaci yau. Ya yiwu membobin kungiyar kasashe masu arzikin man su sami tallafi.

Kasar Azerbaijan da bata cikin kungiyar OPEC ta amince da rage yawan man da take haka, yayinda Rasha tace zata rage yawan mai da take haka cikin shekara ta 2009 idan farashin mai ya ci gaba da faduwa.

Farashin danyen mai ya cira da kasa dad ala daya, inda aka sayar das hi kasa dad ala 44 ganga a kasuwar NY yau.

XS
SM
MD
LG