Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mr.Obama Ya Zabi Babban Jami'i Mai Kula Da Ofishin Kasafin Kudi


Shugaban Amurka mai jiran gado Barak Obama ya zaɓi jami’in da zai gudanar da kasafin kuɗin ƙasar. Mr. Obama ya sanar da Peter Orszag a matsayin shugaban ofishin gudanarwa na kasafin kuɗi, ya kuma umurce shi da ya yi tattalin kuɗin gwamnati ta wajen kawar da ayyukan da basu da sauran amfani.

Sabon shugaban ƙasan yace yiwa tsarin kasafin kuɗi garambawul yana da muhimmanci a wannan lokaci da ake fama da giɓin kasafin kuɗi da kuma koma bayan tattalin arziki.

Tun farko jami’an gwamnatin shugaba Bush sun sanar da wani sabon shirin tallafawa kasuwannin saida gidaje dake fama da koma baya, wani abinda ya ƙara haddasa taɓarɓarcewar tattalin arziki.

XS
SM
MD
LG