Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Pakistan Da Majalisar Dinkin Duniya Zasu Fara Binciken Makasan Bhutto


Wata kakakin Majalisar Dinkin Duniya, tace sabon Prime Ministan Pakistan ya taso da maganar yiwuwar Majalisar Dinkin Duniya ta kafa binciken sanadiyyar kisan gillar da aka yiwa marigayiya Banazir Bhutto.

Michele Montas tace Prime Ministan ya dago wannan magana ne a wata tattaunawa da suka yi ta wayar tarho, da Sakatare Janar na majalisar Dinkin Duniya, ban Ki-moon a jiya Laraba.

Tace amma Majalisar zata bukaci rubutacciyar takardar bukatar kaddamar da binciken daga Pakistan, kafin ma a fara tunanin kafa hukumar binciken, kuma a iya saninta, ba a rubuta wannan takarda ba tukuna.

A jiya Laraba ma, wata kotu a birnin Karachi, ta umarci jami’an gidanb yarin birnin, su saki wani da ake zargi da kasancewa dan Alkaida, wanda aka ce ana zargi da hannu a yunkurin farko na kashe Mrs. Bhutto, saboda rashin wadatacciyar shaida.

XS
SM
MD
LG