Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Paparoma Ya Fara Ziyarar Kwana Hudu A Turkiyya


A ranar farko ta ziyararsa zuwa Turkiyya, Paparoma Benedict yayi kiran da a sami cikakken ‘yancin addini, ya kuma ce hanya mafi inganci ta samun fahimtar juna tsakanin Kiristoci da Musulmi, ita ce tattaunawa.

Kamar yadda Wakiliyar Muryar Amurka Sabina Castelfranco ta ruwaito mana daga birnin Istanbul, bayan Paparoman yayi taro da Shugaban Sashen Al’amuran Addini, Ali Bardakoglu, ya jadda cewa samar da ‘yancin addini shine ginshikin adalci ga jama’a.

Paproman yace Kiristoci da Musulmi ai jikokin mutum daya ne, kuma dukkansu sun yarda da kadaicin Allah. Suna dai bin tafarkin al’adu dabam-dabam ne wajen kira i zuwa tafarkin Allah.

“Wannan shine jigon mutunta juna da muke yi, da kuma ganin kimar kowa. Wamman shine ginshikin hadin kai da fahimta juna a wajen bautawa mahaliccinmu da al’ummarmu.”

Paparoman yace habakar ko wanne irin addini ta dogara ne a kan zaman lafiya. Yace babban dalilinsa na ziyartar Turkiyya, shine samara da hanyar tattaunawa da fahimtar juna, tsakanin al’adu mabambanta.

Da ya ke Magana kan kalamin da Paparoman ya taba yi a Jamus a watan shekaran jiya, wanda ya bata ran musulmin duniya, Jagoran Musulmi Ali bardakoglu yace babban abin dake bata ran musulmin duniya, shine imanin da mutanen yammacin turai suka yi, cewar addinin musulunci da takobi ya yadu a duniya, da kuma mummunar fahimtar da suka yiwa addinin.

Jagoran na musulmi yace musulunci ya kyamaci ta’addanci. Har yanzu musulmi da dama na fushi da kalaman Paparoman, musamman ganin har yanzu bai nemi cikakkiyar afuwa ba. An dai yi ta zanga-zangar kyamar ziyarar tasa tsakanin jiya litinin da yau.

XS
SM
MD
LG