Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Paul Wolfowitz Ya Sauka Daga Mukaminsa


Paul Wolfowitz, dan shekaru 63, ya aje mukaminsa ne sakamakon samunsa da wani kwamitin bincike yayi da laifin sabawa ka’idojin Bankin Duniya, lokacin da ya yiwa wata budurwarsa ma’aikaciyar bankin, karin girma da albashi mai gauni.

Jami’an bankin sun baiyana amincewar Wolfiwitz ya ajiye mukamin nasa ranar Alhamis, bayan sunyi wani taro inda suka duba zabin da ya dace, tsakanin korarsa kai tsaye ko kuma a bashi dama ya sauka da kansa.

Bayanin da ya fito daga bankin yace Wolfowitz zai bar mukamin nasa daga karshen watan gobe na Yuni. Fadar White House tace Shugaba Bush zai baiyana sunan wanda zai gaji Wolfowitz nan bada dadewa ba.

Tun da fari, Shugaba Bush ya baiyana takaicunsa da wannan abin kunya, a wani taron manema labarai da suka yi tare da Prime Ministan Ingila Tony Blair, wanda ke yin wata ziyara zuwa Amurka.

Koda yake dai ya baiwa Wolfowitz cikakken goyon baya a lokacin da yake fafutukar rike mukaminsa, Mr. Bush yace baiji dadin yadda wannan takaddama ta kare ba.

Wani kwamiti na musamman da ya binciki halaiyar Wolfowitz, yace shugaban mai barin gado ya sabawa ka’idoji da dokokin aikinsa, lokacin da ya tsara karin albashi da karin girma ga wata budurwarsa dake aiki a bankin.

Manema labarai dai sun ruwaito cewa Wolfowitz yana kokarin manyan jami’an bankin su sassauta tuhumar rashi da’a da ake masa, shi kuma ya ajiye aikin nasa salin alin. Ilahirin jami’an dake wakiltar Kasashen Turai a Bankin, sun dage dole sai Wolfowitz ya sauka, a yayin da Amurka da Japan suka goyi bayansa.

XS
SM
MD
LG