Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kamfanin Safarar Jirage Ruwa Mafi Girma A Duniya Yace Zai Kaucewa Mashigin Ruwan Aden.


Daya daga cikin kamfanonin safarar jiragen ruwa mafi girma a Duniya,yace jiragensa zasu fara kaucewa mashigin ruwan Aden a saboda barazanar 'yan fashin jirage na Somaliya.

A yau Alhamis Kamfanin A.O.Moller-Maersk yace jiragen ruwan da ba su da saurin tafiyar da zasu iya tserewa 'yan fashin,zasu sake hanyar da suke bi daga kuriyar kudancin Afirka.

Jakadan kasar Rasha a NATO,Dmitry Rogozin, a yau Alhamis yayi kiran da kasashen Duniya su had kai su kai farmaki a kan tungayen 'yan fashin a bakin tekun Somaliya.

A halin da ake ciki, kasashen dake makwabtaka da Bahar Maliya sun yi taron gaggawa domin tattauna yadda zasu yaki hare-haren dake ƙaruwa na 'yan fashi cikin teku a yankin. Masar da Yemen suka kira da a yi taron na yau alhamis kwanaki kadan bayan da aka yi fashin wani makeken jirgin ruwan daukar mai na Sa'udiyya dake cike da mai.

Wakilan gwamnatin wucin gadi ta Somaliya da Sa'udiyya da Sudan da Hadaddiyar daular Larabawa da Djibouti da kuma Jordan sun shiga tattaunawar da aka yi yau a al-Qahira.

Hukumar kula da zirga zirgar jiragen ruwa ta duniya ta ce 'yan fashi na Somaliya sun kai hari kan jirage kusan 100 a wannan shekara, suka yi fashin akalla 36 daga cikinsu. 'Yan fashin sun samu miliyoyin daloli daga kudaden diyyar da ake biyansu.

XS
SM
MD
LG