Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rigingimu Sunci Gaba A Kenya: Amurka Ta Janye Taya Murnarta


Gidan Talbijin na KTN yace an kashe mutum 124 a tashe-tashen hankulan da a halin yanzu suka mamaye biranen Kenya, sakamakon zargin tafka magudin da ya baiwa Shugaba Mwai Kibaki damar yin tazarce.

Shi kansa Mr. Odinga, tare da Shugaba Mwai Kibaki duk sun bukaci jama’a da su kwantar da hankulansu, amm Mr. Odinga yace yana da tabbatacciyar hujjar cewa Kibaki da magoya bayansa sun tafka magudi, inda suka rika karawa Kibaki kuri’u na bogi. A ranar Lahadi Hukumar Zaben kasar ta ayyana Shugaba Mwai Kibaki a matsayin wanda ya lashe zaben, inda ya dara Kibaki da kuri’u dubu 230 kawai.

Odinga ya soke wani taron gangami da ya shirya a tsakiyar birnin Nairobi, bayan gwamnati ka ki ta bada izinin a gudanar dashi, ta kuma tura ‘yan sanda suka mamaye wajen. A maimakon haka, ya ayyana ranar Alhamis a matsayin ranar alhini, inda ya umarci magoya bayansa su daura bakin kyalle a damatsansu domin nuna fushinsu da magudin.

Wadannan tashe tashen hankula sun jefa Kenya cikin yamutsin da bata taba shigarsa ba tun da ta ta sami ‘yancin mulkin kanta daga Birtaniya a shekarar 1963. Tunda Odinga bashi da niyyar saduda, akwai tsoron wannan hautsini zai iya rikidewa ya zama na kabilanci, tsakanin ‘yan kabilar Luo masu goyon bayan Odinga, da Kikuyu, masu goyon bayan Kibaki.

Masu lura da yadda aka gudanar da zaben dai duk sun amince cewa akwai alamun magudi a zaben. Kungiyar Taraiyar Turai tace akwai kwararan shaidu dake nuna cewa anyi murdiya, sannan wata kungiyar masu duba zaben na cikin gida, KEDOF, tace Hukumar Zabe taki ta saurari koke koken jama’a kafin ta baiyana sakamakon zaben.

Dan takarar da ya zo na uku, Kalonzo Musyoka yayi kiran da a kwantar da hankula. Ya kuma ce a karbi sakamakon zaben, duk kuwa da ‘yan korafe korafen da ake dasu.

A yau dai Ma’aikatar Tsaron Amurka ta sauya manufarta ta taya Shugaba Mwai kibaki murnar lashe zaben da tayi a jiya Lahadi. A yau Litinin, Ofishin Jakadancin Amurka a Nairobi ya bayar da wata sanarwa, inda ta nuna damuwarta da matsalolin da aka fuskanta lokacin kidayar kuri’un.

XS
SM
MD
LG