Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojoji Sun Isa Jos Domin Kwantarda Rikicin Siyasa.


Rahotanni daga Nigeria na cewa sojin Nigeria sun isa birnin Jos domin ƙoƙarta kashe rikicin ƙabilanci da addinin dake neman kunno kai inda har aka kashe aƙalla mutane huɗu. Hukumomin Plateau sun kafa doka hana yawon dare yau Juma’a bayan ɓarkewar rikicin dake neman watsuwa a tsakanin Kirista da Musulmi mazauna birnin Jos da kewaye a dalilin sakamakon zaɓen majalisun ƙananan hukumomi. Ya zuwa yanzu dai ba’a fayyace yawan ɓarnar da rikicin ya haifar ba,amma dai an ƙoƙona Masallatai da mujami’u. Akwai ƙarin bayani bayan labarun duniya.

XS
SM
MD
LG