Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sakamakon Zabe Na Farko Farko Da Akayi a Zimbabwe Yana Nunin Kunnen Doki Tsakanin Gwamnati Da Masu Hamayya


Sakamakon farko farko daga Hukumar zabe ta Zimbabwe yana nunin cewa a halin yanzu ana kunnen doki tsakanin Gwamnati mai ci da Jam’iyyar hamayya a zaben Majalisar Dokokin kasar.

Hukumar zabe ta Zimbabwe litinin tace Jam’iyyar shugaba Mugabe, ZANU-PF,da ta masu hamayya MDC, kowacce ta sami kujeru 12 cikin kujeru metan da goma dake Majalisa. Ba a bada sakamakon zaben shugaban kasa ba da aka kammala a karshen mako.

Jam’iyyar MDC ta sake nanata ikirarinta cewa itace ta lashe zaben da aka yi.Jam’iyyar tace nata adadin ya nuna cewa dan takararta Morgan Tsvangirai, yana gaba da kashi 60 cikin dari na kuri’u da aka kada kan abokin takararsa shugaba Robert Mugabe, wadda MDC tace a lisssafinta ya sami kashi talatin cikin dari. Jinkirin bada sakamakon zaben shugaban kasa yasa an soma rade raden ana shirin magudi.

XS
SM
MD
LG