Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sakatariyar Harkokin Wajen Amurka Hillary Clinton Tace Tilas A Ladabtarda Iran


Yau litinin ce Sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton zata isa Saudiyya kan kokarin kasashe dake yammacin Duniya na tsaida shirin nukiliyar Iran,bayan tace tilas a ladabtarda Farisa saboda hankoron mallakar makaman Nukiliya.

Ana sa ran Clinton ta gana da jami’an Saudiyya yau litinin ciki harda sarki Abdullah. Da take magana jiya lahadi a taron hadakar kasashen Islama da Amurka, a Doha a kasar Qatar, Clinton tace Washington tana son a warware rikicin Nukiliyar Iran cikin lumana,amma tace Amurka bazata yi shawarwari daFarisa “yayinda take kera makamin Nukiliya ba”.

Tace Farisa bata baiwa hukumomin kasa da kasa wani zabi ba ,illa aladabtar da ita kuma mai tsanani, saboda matakan takaladatake dauka.

Amurka tana kara matsin lamba ga kwamitin sulhu na MDD ta aza takunkumi kashi na hudu kan Iran saboda taki ta tsaidainganta sinadaran Uranium.

XS
SM
MD
LG