Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sakon Bin Laden Ya Kara Tabbatar Kasancewarsa A Raye


A cikin sakon da Usama Bin Laden ya aike wa da Amurkawa, ya bukacesu da suyi watsi da akidarsu ta dimokradiyya, su rungumi Islama, in dai suna da burin kawo karshen zaman Amurka a Iraq.

Shugaban na Alkaida, yayi watsi da akidar dimokradiyya, wadda yace ba wani ke cin nmoriyarta ba, illa manyan kamfanonin Amurka da na sauran kasashen duniya. Ya kuma soki tsarin tattalin arziki na Jari Hujja, da hade bakin tattalin arzikin duniya, da sauran akidojin yammacin Turai.

Masu nazarin wannan sako sun baiyana shi da cewa, sako ne da lafazinsa ke goyon bayan akidar markisanci, ko kuma gurguzu.

Bin Laden yayi kimanin minti 30 yana magana ba tare da tsayawa ba, inda ya tabo al’amuran baya-bayannan dake faruwa a Amurka sa sauran sassan duniya, abin da yasa masu nazari sukai amannar cewa a ‘yan makonnin nan aka dauki sakon.

Wannan sako da aka aike dashi ta wani dandalin yanar gizo na addinin musulunci, ya nuna cewa an aiko shi ne da nufin bikin cika shekaru shida da harin nan na 11 ga watan Satumba, da aka kaiwa Amurka.

Amurka dai ta bada tayin la'adar dollar Miliyan 25 ga duk wanda ya taimaka aka kama Bin Laden ko mataimakinsa, Aiman Al Zawahiri.

XS
SM
MD
LG