Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shirye Shiryen Rantsar Da Obama Sunyi Nisa


A yau Litinin Shugaban Amurka mai jiran gado, Barack Obama ya yabi mai fafutukar kwatar 'yancin dan adam dinnan na Amurka, Martin Luther King Junior, saboda fifikon da ya bayar kan aikin jama'a.

Yau ranar hutu ce a nan Amurka, wadda aka ware domin karrama Martin Luther King, wadda kuma ake amfanim da ita wajen karfafa guiwar aikin gayya.

A jiya Lahadi ma, Obama ya halarci bukukuwan share fagen kaddamar da shi a matsayin Shugaban Kasa na 44, inda ya kai ziyara zuwa makabartar soji domin karrama sojojin da suka sadaukar da rayukansu ga Amurka.

Daga baya kuma ya halarci wani bikin kade-kade da raye-raye da dubban mutane suka halarta.


XS
SM
MD
LG