Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Barack Obama Ya Gabatarda Jwabin Rahoton Hali Da Kasa Ke Ciki Na Farko Tun Kama Aikinsa


Shugaban Amurka Barack Obama ya yi kira ga majalisun dokokin Amurka su yi aiki kan muhimman bukatun cikin gida da gwamnatinsa ta sa gaba,kamar kiwon lafiya da kuma tattalin arziki, a jAwabinsa na farko da ake kira state of the Union, a turance, ko rahoton hali da kasa take ciki na shekara shekara da ya gabatar.

Da yake magana a zaman hadin guiwar majalisar wakilai data dattijai a daren jiya laraba,Mr. Obama ya yi kiraga majalisa ba tareda bata lokaci ba ta tura masa dokar samar da aikin yi. Saboda haka yace, "batun aiki shine burinmu na farko cikin wan nan shekara ta 2010,shi yasa nake kira a wan daren, na kafa sabuwar dokar samar da ayyukan yi". Haka kuma yayi kira da aza sabon harsashi na ci gaban tattalin arziki dake hangen gaba,saboda tinkarar matsalolin tattalin arziki da Amurkawa suke fuskanta.

Mr. Obama ya lashi takobin ci gaba da yaki na garambawul ga kiwon lafiya,yana mai cewa idan majalisa bata amince da kudurin ba,kudin Inshora zai kara tashi,kuma gibin kasafin kudi zai kara haurawa.

Sabon Gwamnan Virginia, Bob McDonnell, dan republican shi ne ya maida martani a madadin jam’iyyarsa ta Republican. Yace gwamnatin tarayya tana neman daukan abinda ya fi karfinta,sakamakon haka zata baral’uma mai zuwa da dumbin bashi.

XS
SM
MD
LG