Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Boni Yayi Na Benin Ya Gana Da Shugaba Bush


Alhamis dinnan Shugaba George W. Bush ya gana da shugaba Boni Yayi na Jumhuriyar Benin, a Fadar White House.

Tattaunawar tasu dai tayi nazarin irin rawar da kasar Benin, dake yammacin Afirka zata taka game da wadansu muhimman batutuwa da suka shafi yankin. Batutuwan dai sun hada da na Tsaro, Salon Mulkin Dimokradiyya da harkokin lafiya.

Fadar ta White House tace hakika shugabannin biyu sun duba batun hadin kai domin yakar kwayoyin cutar HIV dake haddasa-kanjamau, da fasalin sabon yakin da ake shirin yi da zazzabin cizon sauro, wato Malariya. Sakatariyar harkokin wajen Amurka Condolizza Rice ma tana cikin wannan tattaunawa.

A farkon wannan wata Amurka ta yabawa Jamhuriyar Benin a kan nasararta wajen aiwatar da sabbin tsare tsaren tattalin arzikin kasar, wanda tuni ma har ya fara jawo hankalin masu zuba jari daga kasashen waje.

XS
SM
MD
LG