Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Bush Na Shirin Kara yawan Sojojin Amurka A Iraqi


Ana sa ran Shugaba Bush zai baiyana shirinsa na tura karin sojoji dubu 20 zuwa Iraqi, a jawabin da zai yiwa jama’ar kasa, da daren nan.

Rahotanni dai na nuna cewa yawancin dakarun za a tura su birnin Bagadaza ne, domin su kawo karshen tashe tashen hankulan da ake fama dasu a can. An jiyo Jami’an gwamnati suna cewa Shugaba Bush zai yi umarnin da a mika harkokin tsaron dukkan sassan Iraqi a watan Nuwamba.

Ana kuam sa ran zai baiyana gudunmawar gina kasa ta dola miliyan dubu daya ga kasar ta Iraqi. ‘Yan majalisar Democrat, wadanda suka karbe rinjaye a majalisun Dattawa da Wakilai, sun baiyana adawarsu ga duk wani karin yawan sojojin Amurka a Iraqi.

Wasu daga cikin ‘yan majalisar sunce zasu gabatar da wani kuduri da zai hana duk wani yunkuri na abin da suka kira kara dagula wannan rikici.

XS
SM
MD
LG