Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Musharraf Zai Tube Khaki Ranar Alhamis


Manyan Jami’an Kasar Pakistan sunce Shugaba Pervez Musharraf zai yi murabus daga mukamin Shugaban Rundunar Sojin kasar, ya kuma saba laya a matsayin Sabon Shugaban Kasa na dimokradiyya a ranar Alhamis mai zuwa.

Kakakin Shugaba Musharraf Rashid Qureishi ne yayi wannan bayani ga wadansu kafofin yada labarai a yau Litinin. Kakakin Rundunar Sojin Kasar, Manjo Janar wahid Arshad shima ya bada irin wannan sanarwa ga wadansu kafofin yada labaran. A makon da ya gabata wasu manyan jami’an gwamnatin Pakistan suka yi irin wannan hasashe, inda suka ce Janar Musharraf zai aje mukaminsa na soja a ‘yan kwanankin baya.

Shugaba Musharraf dai ya sha iza wutar kasashen duniya kan ya ajiye mukaminsa na soja, in dai har da gaske yake dimokradiyyar tasa.

A yau Litinin kuma tsohon Prime Minista Nawaz Sharif yayi rijistar tsayawa takarar shiga majalisar dokokin kasar da za a gudanar ranar takwas ga watan Janiru. ‘Yan sa’o’i kadan kafin a zayyana sunan nasa, Nawaz Sharif ya lashi takobin watsi da duk wani zawarcisa da za a yi na yazo a kafa gwamnatin hadin guiwa.

A jiya Lahadi Mr. Sharif ya sauka a Lahore, daga saudi Arabiya, inda yayi zaman gudun hijira har na tsawon shekaru bakwai. A jiyan abokiyar adawarsa Mrs. Benazir Bhutto, jiya ta shigar da nata takardun.

XS
SM
MD
LG