Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba  Robert Mugabe Ya Bukaci Yan Kasuwa Cikin Kasar Su Rage Kudin Kaya


Shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe yana neman a yi rangwami kan kayan masarufi da harkokin rayuwa, ’yan kwanaki kafin babban zaben da za a gudanar a kasar.

A cikin jawabin da kafofin sadarwa suka yayata, Mr Mugabe yace yana son ’yan kasuwa su rage kudin hajarsu zuwa yadda suke kafin sha biyu ga watan Fabrairu lokacinda aka karawa ma’aikata albashi. Shugaban ya dora laifin tsadar rayuwa da ta tashi da tsakanin kashi dari bisa dari zuwa dubu bisa dari kan abokan hamayya da yace suna neman canjin gwamnati.

Yace gwamnati zata iya kwace kamfanonin da suka ki rage kudin hajarsu. Mr. Mugabe yana takara karo na shidda a matsayin shugaban kasa a zaben da za a gudanar ranar Asabar.

Cikin wadanda zasu kara dashi a zaben mai zuwa harda wani tsohon memban Jam’iya mai mulki, Simba Makoni,da kuma dadadden shugaban hamayya Morgan Tsvangirai.

Jiya Litinin ce Jam’iyar Hamayya, Movement for Democratic Change, ta zargi gwamnatin da niyar yin magudi.

XS
SM
MD
LG