Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Wade Yayi Galaba A zaben Senegal


Hukumomi a kasar Senegal sun tabbatar da cewa Shugaban kasar, Wbdullahi Wade, shine ya lashe babban zaben kasar da aka gudanar ranar lahadin da ta gabata.

Sakamakon wucin gadi da aka bayar a yau Alhamis, ya nuna cewa Shugaba Wade ya lashe kusan kashi 56 bisa dari na kuri’un da aka kada. Wannan ya nuna babu bukatar komawa zagaye na biyu.

Abin da ya rage yanzu shine Babbar kotun Kasar ta Senegal ta amince da sakamakon zaben, kafin a tabbatar dashi a matsayin sahihi.

Prime Minista Idrissa Seck, wanda ya zo na biyu, ya sami kashi 15 bisa dari na kuri’un. Masu lura da zaben daga kasashen yankin sunce an gudanar da wannan zabe cikin gaskiya, kuma babu watat almundahana.

Saidai jam’iyyar gurguzu ta ‘yan adawa ta soki sakamakon, inda tace an tafka magudi, domin kuwa wadansu sun kada kuri’u fiye da sau daya. Ta dai ce zata kalubalanci sakamakon.

Mr. Wade, mai shekaru 80 da ‘yan kai, ya dare kan ragamar mulkin kasar tun da ya lashe babban zaben kasar na shekara ta 2000.

XS
SM
MD
LG