Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Alumar Tibet Dalai Lama Yace A shirye yake Ya Tattauna Da Shugabannin China


Shugaban al’ummar yankin Tibet Dalai lama yace a shirye yake da ya zauna a tattauna da shugabannin kasar China game da matsalolin Tibet, zai kuma yi na’am idan tattaunawar zata hada da shugaba Hu Jintao na China da zarar an kammala zanga-zangar nuna kymar da ake yiwa manufofin Gwamnatin China a Tibet.

A wata ganawar da limamin Budda dake gudun mafaka yayi da manema labarai dazu da hantsi, yace duk da cewar a yanzu dai ba zai iya wani bulaguron zuwa birnin Beijing ba amma zai kokarta zuwa domin hakan ya zama wata alamar dake nuna karfafa mutunci da neman zaman lafiyar al’ummar Tibet.

Sai dai Gwamnatin China na zargin Dalai lama da laifin zama kanwa uwar gamin tarzomar da yanzu ake yi a yankin Tibet, harma gwamnatin China ta amince da cewar zanga-zangar ta watsu zuwa wasu lardunan China.

XS
SM
MD
LG