Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Amurka Barack Obama Ya Gabatar Da Kasafin Kudi Na Shekara Mai Zuwa


Jiya Litinin shugaban Amurka Barack Obama ya gabatar da kasafin kudin gwamnatin tarayya na dala zambar uku da miliyan dubu dari takwas abinda zai sa a sami gibi na dala zambar daya da miliyan dubu shida bana.

Kasafin kudin ya kunshi dala miliyan dubu dari da za a kashe kan samar da sababbin ayyuka domin shawo kan matsalar rashin aikin yi da ya haura kashi goma bisa dari. Kasafin kudin ya tanada Kara kashe kudin kan ayyukan soja da kuma harkokin ilimi. Sai dai Mr. Obama ya ci alwashin yin aiki tukuru domin ganin an rage gibi da kimanin rabi zamanin mulkinsa, ta wajen karawa Amurkawa masu arziki haraji da kuma rage yawan kudin da ake kashewa a cikin gida.

Shugaba Obama ya shaidawa manema labarai a fadar White House cewa, “ba zamu ci gaba da kashe kudi sai kace gibi bata da illa ba.” Idan majalisa ta amince da kasafin kudin, za a fara aiki da shi ranar daya ga watan Oktoba shekarar kudi ta bana.

Sai dai ‘yan hamayya na jam’iyar Republican basu yi wata wata ba, suka fara kushewa kasafin kudin. Shugaban jam’iyar Republican a majalisar dattijai, Mitch McConell, yace kasafin kudin yana nuna kudin da za a kashe zai karu, za a kuma kara yawan haraji da kuma tsunduma cikin bashi. A halin da ake ciki kuma, wan nan kasafin kudi da shugaba Barack Obama ya gabatar shine mafi girma a tarihi na dala miliyan dubu dari bakwai da takwas ga bangaren tsaro, da nufin ganin nasarar yakin Iraq da Afghanistan.

Za a kuma yi amfani da kudin wajen horas da dakarun Amurka domin duk wani rikicin da zai taso a kasashen duniya da sauran manyan shugabannin yankuna ko kungiyoyin ta’addanci. Bisa ga cewar sakataren tsaron Amurka Robert Gates, Amurka tana bukatar zama da shiri sabili da lokuta na gaba dake cike da hatsari wadda kuma bata da tabbas.

XS
SM
MD
LG