Shugaban Kasar Somalia Abdullahi Yusuf, ya nada sabon Prime Minista a yau Talata, duk kuwa da rashin amincewar Majalisa da korar da ya yiwa wanda ke rike da wannan mukami a halin yanzu.
Shugaban ya nada
wani babban bafadensa Mohammed Mahmoud Guled, domin ya maye gurbin Nur Hassan
Hussein.
Nan take
Gwamnatin kasar Kenya, wadda ke kokarin sulhunta tsakanin jama’ar kasar, tayi
watsi da wannan mataki. Ministan Harkokin Wajen Kenya, Moses Watangula yace
suna duba hanyoyin kakabawa shugabannin na Somalia takunkumi, ciki har da na
hana zirga-zirga tsakanin kasashen biyu, da kuma kwace wasu kadarorin Somaliyan
dake Kenya.
Kenya tace Mr.
Hussein yayi watsi da wannan kora, kuma yayi zamansa daran a kan kujerar ta
Prime Minista.
Mr Hussein ya
sami gagrumin goyon baya daga ‘yan Majalisar Kenyta, bayan da Shugaban yace zai
kore shi saboda zargin rashawa da rashin iya gudanar da aiki.