Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Yan Bangar Mahdi Muqtada alSadr Ya Umurci Magoya Bayansa Dasu Ajiye Makamai A Fafatawa Da Sukeyi Da Dakarun Gwamnati


Gwamantin Iraqi tayi marhabin da umarnin da shehin Malamin’yan mashabar shi’a Muqtda al-Sadr, ya baiwa mayakan sakai dake biyayya gareshi su janye kan tituna daga artabu da suke gwabzawa da Jami’an tsaron kasar,a kokarinsa na tilastawa hukumomin kasar su kawo karshen farmaki da suke kaiwa a Basra da wasu tungugoin magoya bayan shi Sadr.

Ahalin yanzu kuma shaidun gani da ido sunce anyi luguden rokoki da kwansan bom kan yankin nan mai ji da tsaro fiye da ko ina a Bagadaza,da ake kira Green Zone,inda nanne Ofishin Jakdancin Amurka da Sakatariat din Gwamnatin Iraqi suke.Babu rahoto nan take gameda hasarar rayuka ko jikkata a harin na yau litinin.Amma jerin hare hare na baya bayan nan kan wannan yanki ya kashe akalla Amurkawa biyu cikin mako da ya shige.

Harin na yau ya zo ne kwana guda bayanda Malamin ‘yan shi’an Muqtada al-sadr ya umurci mayakan sakai dake biyayya gareshi su janye daga mummunar bata kashi da suke yi da dakarun Gwamnati dana rundunar kwance. Kakakin Malamain,Hazem al-Aaraji,yace Sadr ya bada umurnin tsagaiata wutan ne jiya lahadi, domin kawo karshen zubda jinin ‘yan Iraqi.

XS
SM
MD
LG