Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabannin Kasashen Asiya Da Turai Sun Lashi Takobin Kare Tattalin Arzikinsu


A karshen taron kolin da suka kamalla jiya a birnin Beijing ta China, shugabannin kasashen Asia da Turai sun ce sun daura damarar zare dantsen hana tabarbarewar arzikin dake barazana ga kasashe da dama na duniyarn nan.

A cikin sanarwar hadin guiwa da suka bada, wadanan kasashen 40 dake cikin kungiyar hadin kan kasashen Asia/Turai sunce zasu dauki kwararan matakan chanja hanyoyin gudanarda harakokin yau da kullum na kudade.

A lokacin taron ne, mai masaukinsu, firimiyan kasar ta China, Wan Jiabao yace koda yake kasarshi ta Sin na farin cikin ganin yadda kasashe suka tasarwa wannan matsalar tsaye, yana ganin akwai bukatar daukan Karin matakai.

Dangane da hakan ne shima shugaba George Bush na Amurka yake kira akan kasashen duniya da su kara hakuri kan halin da aka shiga, ya kuma yi kira a kansu da su dada daukan matakan tabattarda cewa sun bar kasuwanninsu a bude.

Ran 15 ga watan Nuwambar nan mai zuwa ne dai shugaba Bush zaib vdauki bakuncin taron kolin kungiyar nan ta kasashe 20 da ake kira G-20, a nan Washington.

XS
SM
MD
LG