Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Siyasar Amurka Tana Kara zafi


Muhawarar tana daya daga cikin muhimman al'amuran zaben kasar da ake shirin gudanarwa a watan gobe.

Sanata Obama yayi yakin neman zabensa ne a jihar Indiana, jihar da jam'iyyar Republican take da karfi a zaben shugaban kasa. Obama ya dora alhakin raunin tattalin arzikin amurka a kan gwamnati mai barin gado ta Shugaba Bush, ya kuma yi alkawarin jagorancin kwarai idan aka zabe shi. Obama yace Sen McCain dan takarar jam'iya mai mulki ta Republican da mataimakiyarsa Gwamnar jihar Alaska Sarah Palin, suna amfani da salon kamfe na bata suna ne domin kawai dauke hankalin amurkawa daga kan matsalar tattalin arzikin kasar.

McCain da Palin sun shafe wunin jiya a jihar Pennsylvania dake Arewa maso Gabashin Amurka, inda McCain ya bayyana shakku kan halayyar Obama. McCain yace Obama zai goyi bayan facaka da kudin gwamnati idan aka zabeshi, yayinda ya riga ya nemi a kashe sama da dala miliyan dubu dari a farkon shekara da kuma goyon bayan kashe kudi kan ayyukan da wadansu `yan majalisa suke nema a aiwatar cikin shekaru uku da ya shafe a matsayin saneta.

Daga baya McCain da Palin suka isa jihar Ohio, wata jihar mai matukar muhimmanci a zaben na shugaban kasa.

XS
SM
MD
LG