Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojoji Suna Ci Gaba Da Sintiri A Jos Da Kewaye


Rundunar sojin Nigeria na ci gaba da sintiri a kan titunan birnin Jos, jihar Plateau domin tarfa ruwa a wutar rikicin dake ci tsakanin matasan Kirista da Musulmi. Rahotanni na cewa al’amura sun fara lafawa domin an sami sassafcin lokutan aiki da dokar hana yawo saboda lafawar rikicin jiya laraba.

Shaidun gani da ido sun ce rikicin ya watsu zuwa yankin gefen birnin Jos inda yanzu haka jami’an tsaron ke kokarin cin dungumin rikicin. Shugabannin Kirista da na Musulmi sun ce mutane sama da metan ne suka halaka, amma jami’an Gwamnati sun ce mutane sittin ne. kungiyar kare mutuncin Bil Adama ta Human Rights, tace akalla mutane sama da dari biyar ne suka yi asarar gidajensu na kwana.

Babban Magatakardar MDD Ban Ki-moon yace barkewar sabon rikicin na Jos nada matukar damuwa don haka yake kira ga shugabannin Addini da na siyasar Nigeria da su kokarta daukan matakin kawo karshen rikicin kabilanci da addini a Nigeria domin Nigeria ta sami ci gaba a tattalin arzikin kasa.

XS
SM
MD
LG