Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojoji Sunyi Tabargaza A Guinea Ta Conakry 


Wani dan jarida mazaunin Guinea, Maseco Conde, yace haka kwatsam sai murnar sojojin bayan an baiyana korar manyan jami’an sojin kasar ta sauya zuwa fushi, saboda sunce koda yake an cika alkawarin sauke manyan jami’an sojin, ba a cika masu alkawarin tattaunawa dasu ba.

Conde yace sojojin sun farfasa kantuna da rumbunan adana kayan masarufi a unguwar Matam dake bayan garin Conakry, suka saci shinkafa da sauran kayan masarufi. An dai ci gaba da harbe harbe har zuwa tsakara dare, kuma an jiwa mutane da dama raunuka.

Kimanin sati biyu kenan sojojin suna ta harbe harbe a sama, suna neman a sauke manyan jami’an sojin kasar, a kayautata yanayin rayuwarsu, a kuma biyasu albashin da suke bin bashi, tare da karin girma. Jiya Lahadi shugaba Conte ya sauke wasu manyan jami’an sojin kasar, cikinsu har da Ministan tsaro, Arafan Camara.

Conde yace a yayin da wasu sojojin ke farin ciki da wannan al’amari, wasu kuwa cewa sukai ba zasu amince da wadanda aka nada su maye gurbin tsofaffin shugabannin ba. Conde yace wani rukunin sojojin sunki su amince da nadin Muhammadu Bailo Diallo, wani tsohon hafsan soji, a matsayin Ministan Tsaro, saboda sunce yana da tabon rashawa a tare da shi.

Sojojin Guinea dai sun taimaka kwarai wajen dorewar gwamnatin Shugaba Conte a kan karagar mulki, musamman ma lokacin da aka yi wani kazamin yajin aikin ma’aikata a farkon shekarar nan.

XS
SM
MD
LG