Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Talakawan Burma Sun Shiga Tasku


Ma’aikatan agaji da manema labarai a kasar Burma, sunce dimbin mutanen da guguwar Nargis ta nakasa a Burma, suna ketara kogin Irrawaddy, a fafutukar da suke yi ta neman abinci, ruwan sha da magunguna.

Shaidun gani da ido sunce sunga mutane suna kokawar karbar kayan agaji, a garuruwan da aka iya kaiwa, gefe guda kuma ga gawawwaki nan birjik a cikin kogin, suna yawo a kan ruwa.

A halin da ake ciki, Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-moon ya roki hukumomin kasar Burma da su yiwa Allah, su bada dama masu rabon kayan agaji su shiga kasar domin bayar da tallafi.

Shugaban Hukumar Kula da aikin agaji na majalisar Dinkin Duniya, John Holmes ya gaya wa manema labarai cewa zai yi kyau in da Burma zata janye ka’idojin bayar da takardun visar shiga kasarta, a kalla na wani dan lokaci.

Hukumomin Burma dai na shan suka kan yadda suke ki sassauta ka’idojin shiga ksarsu, al’amarin da ya kara jefa mabukata cikin mawuyacin hali. Saidai Holmes yace suna tattaunawa da gwamnati.

Sakatariyar harkokin Wajen Amurka Condoleezza Rice ma dai ta roki hukumomin na Burma da su kyale ma’aikatan agaji su kai dauki ga mabukatan cikin gaggawa.

XS
SM
MD
LG