Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tarayyar Turai Ta Aike Da Tallafi Ga Jamhuriyar Afirka Ta Tsakiya


Tarayyar Turai ta aike da dala milyan bakwai da dubu dari biyar tallafi ga Jamhuriyar Afirka ta tsakiya,kasa mafi talauci a Duniya baki daya.

Tarayyar a sanarwa da ta bayar jiya litinin,ta ce ta bada gudumawar ne da nufin tallafawa kimanin ‘yan gudun hijira dubu metan da wasu marasa galihu dake arewacin kasar, yankin da gwamnati take fafatawa da ‘yan tawaye. Sanarwar tace duk da ci gaban siyasa da aka samu a baya bayan nan,lamari a kasar bai tabuka komi ba wajen inganta zamantakewar al’uma a shekara daya da ta shige.

Tarayyar Turan ta ce ba bada agaji ne mafita ga matsaloli da kasar ke fuskanta, maimakon haka, kamata yayi kasar ta dage wajen cimma sulhu,inganta gwamnati,da kuma tsara ayyukan ci gaba na tsawon lokaci. Kasar Jamhuriyar Afirka Ta Tsakiya tun 2005 lokacin da aka zabi shugaban kasa Francois Bozize,take fafatawa da ’yan tawaye. Bozize dai ya zama shugaban kasa a 2003 ne bayan ya jagoranci juyin mulkin soja

XS
SM
MD
LG